Monday, 25 February 2019

Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno


A yayin da a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, mai aukuwar ta auku, an gudanar da babban zabe na kujerar shugaba kasa da ta 'yan majalisun tarayya cikin duk wani kwararo, lungu da sako da ke fadin kasar nan.
Bisa ga madogara ta kiyasi da kuma hasashe, tun a yanzu da yawa daga cikin mafi akasarin 'yan takara masu hankoron madafan iko na kujerun mulki a fadin kasar nan, sun fara sanin makomar su ta samun nasara ko kuma akasin haka.
Tun a jiya da yawa daga cikin sakamakon babban zabe na wasu rumfuna da mazabu a fadin kasar nan ya fara bayyana,


Jihar Kano
Karamar hukumar Tudun Wada
APC: 38,865
PDP: 10,707
Karamar hukumar Tsanyawa
APC: 25,823
PDP: 5,399
Karamar hukumar Sumaila
APC: 34,609
PDP: 4,904
Karamar hukumar Gwarzo
APC: 33,581
PDP: 10,638
Karamar hukumar Rano
APC: 23,855
PDP: 7,055
Karamar hukumar Ajingi
APC: 21,458
PDP: 5,267
Karamar hukumar Gezawa
APC: 29,954
PDP: 8,246
Karamar hukumar Bebeji
APC: 26,023
PDP: 8,190
Karamar hukumar Gaya
APC: 25,864
PDP: 6,577
Karamar hukumar Albasu
APC: 19,073
PDP: 6,101
Karamar hukumar Warawa
APC: 19,073
PDP: 6,101
Karamar hukumar Kunci
APC: 20,375
PDP: 4,983
Karamar hukumar Bagwai
APC: 23,375
PDP: 10,584
Karamar hukumar Doguwa
APC:25,454
PDP: 7,031
Karamar hukumar Garko
APC: 22,356
PDP: 2,840
Karamar hukumar Kabo
APC: 29,482
PDP: 8,955
Karamar hukumar Danbatta
APC: 31,850
PDP: 6,947
Karamar hukumar Wudil
APC: 28,755
PDP: 5,108
Karamar hukumar Bichi
APC: 42,714
PDP: 11,050
Karamar hukumar Minjibir
APC: 22,725
PDP: 2,840
Sakamakon zaben kujerar shugaban kasa daga karamar hukumar Gabasawa
APC: 24,420
PDP: 6,130
Karamar hukumar Bagwai
APC: 23,375
PDP: 10,583
A yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, mun samu cewa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya fidda shugaban kasa Muhammadu Buhari kunya yayin da ya tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a karamar hukumar Dawakin Tofa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kasancewar ta mahaifar sa, Gwamna Ganduje bai yi sake ba wajen tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a karamar hukumar Dawakin Tofa inda shugaban kasa Buhari ya yi nasara da kimanin kuri'u 37,147.
 Buhari ya yi nisan gaske gami da zarra ta fuskar samun nasara akan babban abokin adawar sa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, inda ya samu kuri'u 6,507 kacal a mahaifar gwamna mai ci a jihar Kano.
Sakamakon zaben shugaban kasa daga karamar hukumar Albasu
APC: 26,412
PDP: 10,285
Karamar hukumar Rimin Gado
APC: 17,999
PDP: 12,665
Karamar hukumar Ungogo
APC: 51,842
PDP: 10,475
Karamar hukumar Bunkure
APC: 27,232
PDP: 9,528
Karamar hukumar Tudun Wada
APC: 38,865
PDP: 10,707
Karamar hukumar Tofa
APC: 15,797
PDP: 10,746
Karamar hukumar Kunchi
APC: 21,556
PDP: 4,937
Karamar hukumar Makoda
APC: 24,749
PDP: 3,234
Karamar hukumar Shanono
APC: 24,232
PDP: 8,182
Karamar hukumar Sumaila
PDP: 34,602
APC: 4,904
Karamar hukumar Gwale
Kujerar shugaban Kasa
APC: 50,834
PDP: 12,283
Kujerar Sanata
APC: 40,352
PDP: 21,117
Majalisar Wakilai
APC: 35,276
PDP: 18,997
Kash! Kamar yadda alkalin zaben Mallam Sani Umar ya bayyana a yau Lahadi, Sanatan shiyyar Kano ta Tsakiya ya gaza fidda kan sa kunya a wurin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Mallam Umar ya zayyana cewa, Atiku ya lashe kuri'u 13,113 yayin da ya sha babban kayi a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takara na jam'iyyar APC, wanda ya samu kuri'u 26, 110 a karamar hukumar Madobi da ta kasance mahaifa ga tsohon gwamna Kano, Kwankwaso.

Dan Majalisar mai wakilcin shiyyar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin na jam'iyyar APC ya sha kyar, inda ya sake samun nasara da kimanin kuri'u, 41,071 yayin da abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, ya samu kuri'u 40, 412.
Abdulmunin Jibrin
Sakamakon zabe daga karamar hukumar Garun Mallam
Kujerar shugaban kasa
APC: 23, 810
PDP: 4,861
Kujerar Sanata
APC: 18,412
PDP: 8,548
Majalisar Wakilai
APC: 18,029
PDP: 8,262
Sakamakon zabe daga karamar hukumar Tofa
Kujerar Shugaban kasa
APC: 19,984
PDP: 7,732
Kujerar Sanatan Kano ta Arewa
APC: 16,794
PDP: 10,746
SDP: 397
Kamar yadda Salihu Tanko Yakasai, hadimin gwamnan jihar Kano akan sabuwar hanyar sadarwar zamani ya bayyana s hafin sa na zauren sada zumunta, mun samu cewa, dan takarar kujerar majalisar wakilai na karamar hukumar Madobi, Hon. Kabiru Idris, ya lashe zaben sa.
Honarabul Kabiru na jam'iyyar APC ya lashe zaben sa da kimanin kuri'u 22,100 a matsayin wakilin kananan hukumomin Kura, Garun Mallam da kuma karamar hukumar Madobi da ta kasance mahaifa ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso.
Jigirya, Kawaji ward, Nasarawa LGA
Kujerar shugaban kasa
APC: 88
PDP: 14
Kujerar Sanata
APC: 76
PDP: 28
Majalisar Wakilai
APC: 69
PDP: 28
PU 017, Jigirya, Kawaji ward, Nasarawa LG
Kujerar shugaban kasa
APC:120
PDP: 22
Kujerar Sanata
APC: 8
PDP: 58
Majalisar Wakilai
APC: 78
PDP: 56
PU 019; Jigirya, Kawaji ward, Nasarawa LGA
Kujerar shugaban kasa
APC: 230
PDP: 39
Kujerar Sanata
APC: 165
PDP: 96
Majalisar Wakilai:
APC: 137
PDP: 47
Mazabar Kwankwaso a garin Madobi
PDP: 156
APC: 72
Jihar Adamawa
Dalla-Dalla yadda sakamakon zaben shugaban kasa tsakanin Buhari da Atiku ya kasance cikin kananan hukumomin jihar Adamawa
Karamar hukumar Hong
APC: 20,471
PDP: 23,039
Karamar hukumar Ganye
APC: 20,360
PDP: 17,770
Karamar hukumar Guyuk
APC: 10,825
PDP: 22,059
Karamar hukumar Lamurde
APC: 8,123
PDP: 21,404
Karamar hukumar Yola South
APC: 34,534
PDP: 20,414
Karamar hukumar Mubi South
APC: 19,361
PDP: 10,514
Karamar hukumar Mubi North
APC: 26,746
PDP: 23,156
Karamar hukumar Shelleng
APC: 13,531
PDP: 11,912
Karamar hukumar Girei
APC: 17,765
PDP: 14,673
Karamar hukumar Yola North
APC: 43,865
PDP: 27,789
Karamar hukumar Numan
APC: 10,610
PDP: 23,469
Karamar hukumar Demsa
APC: 6,989
PDP: 29,997
Karamar hukumar Mayo-Belwa
APC: 20,842
PDP: 23,734
Karamar hukumar Madagali
APC: 8,208
PDP: 14,594
Karamar hukumar Maiha
APC: 17,034
PDP: 7,916
Karamar hukumar Song
APC: 17,350
PDP: 22,648
Karamar hukumar Fufore
APC: 29,507
PDP: 16,430
Karamar hukumar Gombi
APC: 12,805
PDP: 18172
Karamar hukumar Jada
APC: 21,332
PDP: 22,877
Karamar hukumar Michika
APC: 10,669
PDP: 32,085
Karamar hukumar Toungo
APC: 7,145
PDP: 5,614
Jimillar sakamakon zaben jihar Adamawa yayin da nasara ta rinjaya zuwa Atiku
APC: 338,927
PDP: 349,690
Karamar hukumar Madagali
APC: 8,208
PDP: 14,594
Karamar hukumar Maiha
APC: 17,034
PDP: 7,916
Karamar hukumar Song
APC: 29,507
PDP: 16,430
Karamar hukumar Gombi
APC: 12,805
PDP: 18,172
Sakamakon Zabe: Buhari ya lashe zaben karamar hukumar Girei a jihar Adamawa
APC: 17,765
PDP: 14,673
Karamar hukumar Mubi ta Kudu
APC: 19,361
PDP: 10,514
Low Cost PU:016; Lokuwa ward, LG: Mubi North
Kujerar Shugaban kasa
PDP: 156
APC: 78
Ajiya ward (Mazabar Atiku)
APC: 186
PDP: 140
PU:10 Unguwar Mbamoi dake fadar Lamidon Adamawa
APC: 228
PDP: 138
Jihar Yobe
Dalla-Dalla yadda ta kasance a kananan hukumomin jihar Yobe tsakanin Buhari da Atiku
1. Bursari APC 22,253 PDP 2,555
2. Jakusko APC 34,424 PDP 3,390
3. Gulani APC 22,858 PDP 2,612
4. Bade APC 42,485 PDP 3,295
5. Nguru APC 36,433 PDP 5,352
6. Yunusari APC 23,837 PDP 939
7. Potiskum APC 62,101 PDP 4,331
8. Fune APC 43,948 PDP 5,707
9. Yusufari APC 22,157 PDP 3,567
10. Fika APC 42,488 PDP , 5522
11. Geidam APC 16,338 PDP 613
12. Tarmuwa APC 12,122 PDP 1,269
13. Damaturu APC 35,772 PDP 2,099
14. Machina APC 14,619 PDP 2,315
15. Karasuwa APC 22,377 PDP 3,692
16. Gujba APC 12,227 PDP 325
17. Nangere APC 31475 PDP 3180
Karamar hukumar Tarmuwa
APC: 12,122
PDP: 1,269
Karamar hukumar Damaturu
APC: 35,772
PDP: 2,099
Karamar hukumar Karasuwa
APC: 22,377
PDP: 3,692
Karamar hukumar Machina
APC: 14,619
PDP: 2,315
Zaben Kujerar shugaban kasa Karamar hukumar Gujba:
APC: 12,227
PDP: 325
PU: Sabon Layi Pri, School; Code: 012 B; LG: Potiskum RA: Bolewa B, Yobe South Senatorial District
Kujerar shugaban kasa
APC: 265
PDP: 12
Kujerar Sanata
APC: 155
PDP: 116
Majalisar Wakilai
APC: 171
PDP: 101
Sabon Layi Pri, School; Code: 012 A; LG: Potiskum RA: Bolewa B, Yobe South Senatorial District
Kujerar shugaban kasa
APC: 248
PDP: 3
Kujerar Sanata
APC: 152
PDP: 98
Majalisar Wakilai
APC: 179
PDP: 57
Jihar Borno
Sakamakon zaben kujerar shugaban kasa na karamar hukumar Mafa
APC: 50,851
PDP: 138
Zaben kujerar shugaban kasa daga karamar hukumar Magumeri
APC: 12,739
PDP: 694
PU 004, Bale Galtimari Jere
APC: 244
PDP: 32
PU 005, Bale Galtimari Jere
APC: 349
PDP: 35
PU 014, Waziri Babagana, Shehuri South Ward
APC: 200
PDP: 7
PU 023 Kukawa, Lamisula Ward
APC: 190https://hausa.legit.ng/1223861-sakamakon-zabe-daga-jihohin-kano-adamawa-yobe-da-borno.html
PDP: 21
Bakin Kasuwa, garin Shaffa, Hawul LGA
APC: 288
PDP: 3
Mandagirau, Biu LGA
APC: 2590
PDP: 154
Ku ci gaba da kasancewa a kan wannan shafi yayin da muka daura damarar kwararo muku yadda sakamakon zaben ke ci gaba da kasancewa a wannan jihohi biyar da muka wassafa.

Tuesday, 19 February 2019

Kwace akwatin zabe: Sojoji sun sha alwashin bin umarnin Buhari su bindige mutum

Kwace akwatin zabe: Sojoji sun sha alwashin bin umarnin Buhari su bindige mutum

Kwace akwatin zabe: Sojoji sun sha alwashin bin umarnin Buhari su bindige mutum

Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta bi Umarnin Shugaba Muhammadu Buhari, matsawar ya bada odar cewa duk wanda ya fizgi akwatin zabe, to a bindige shi kawai, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hukumar sojin sun yi wannan karin haske ne biyo bayan kakkausan furucin da Buhari ya yi a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu cewa duk wanda ya saci akwatin zabe, to ya yi a ta bakin ran sa.

Wannan kalami na Shugaban kasar a janyo ce-ce-ku-ce , suka da kuma caccaka, duk da dai magoya bayan shugaban na ta kokarin kare dalilan sa na yin furucin.
Dokar zabe dai ta tanadi daurin shekaru biyu ga duk wanda aka kama ya saci akwatin da aka jefa wa kuri’a.

Shi kuma Buhari ya ce a harbe wanda ya saci akwati ya tsere kawai. Ya yi wannan kakkausan kalami ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC jiya Litinin a Abuja.

A na su bangaren, sojojin Najeriya sun kara wa wannan tankiya zafi, yayin da Kakakin su Sagir Musa ya bayyana wa majiyarmu ta Premium imes cewa idan dai shugaban kasa wanda kuma shi ne Babban Kwamandan sojin Najeriya gaba daya, ya bayar da umarni ga sojoji, to babu tantama, ba tababa, kuma babu wani bata lokaci, aiwatarwa kawai za su yi.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa d an takaran kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoplea Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a jiya Litinin, 18 ga watan Fabrairu yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna “kalan shi tare da rashin girmama kundin tsari mulki”, ta hanyar furta cewa a bakin ran duk wanda yayi yunkurin sace akwatin zabe.


Atiku, a wani jawabin da yayi ta hannun kakinsa, Phrank Shaibu, yace barazana da mutuwa ga mutane a halin shirin gudanar da zabe “kalma ce dake hadda sa rikicin zabe”.

Atiku wanda ya nuna rashin amincewarsa akan shirin tura sojoji a zaben 2019, inda yake bayyana hakan a matsayin rashin dacewa ga damokardiyya, yayi Allah wadai da dabarun tsoratarwa da Gwamnatin Tarayya ke shiryawa.
PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari na harbe duk wanda aka kama da satar akwatin zabe – Garba Shehu

PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari na harbe duk wanda aka kama da satar akwatin zabe – Garba Shehu

PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari na harbe duk wanda aka kama da satar akwatin zabe – Garba Shehu

A yau, Talata, ne fadar shugaban kasa ta bayyana cewar jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga halin damuwa bayan shugaban kasa Muhammdu Buhari ya umarci jami’an tsaro da kar su tausaya wa duk wanda ya yi yunkurin gudu wa da akwatin kuri’u a zabukan da za a gudanar cikin watan Fabarairu da Maris.

Fadar shugaban kasa ta ce kalaman shugaba Buhari gargadi ne ga ‘yan siyasar da su ka mayar da satar akwatun kuri’u ta hanyar amfani da ‘yan daba al’ada a lokutan zabe.

Da ya ke Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, babban mai taimaka wa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Garba Shehu, y aba boyayyen abu ba ne cewar wasu ‘yan siyasa na amfani da ‘yan ta’adda domin su sace akwatin kuri’u sannan su kashe ma su kada kuri’a ko kuma su raunata su.

Ya ce shugaba Buhari ya yi kalamin ne domin tabbatar da cewar ba a cutar da ma su kada kuri’a ba lokacin zabe tare da bayyana cewar ya kamata a jinjina wa Buhari bisa wannan gargadi ga ma su niyyar sace akwatin kuri’u a lokutan zabe


Kazalika, ya nuna rashin jin dadin sa bisa sukar Buhari a kan furucin da ya yi a kan ma su niyyar sace akwati, tare da nuna mamaki a kan dalilin damuwar su da kalaman na shugaban kasa.

A cewar Shehu, “ mambobin jam’iyyar adawa, musamman jam’iyyar PDP, ne ke sukar Buhari saboda sun gama shirya yadda za su yi magudin zabe ta hanyar satar akwatin kuri’u .

“ Sun fahimci cewar shugaba Buhari ba zai lamunci almundahanar da su ka saba da ita ba wannan karon. Sun nuna abinda su ke niyyar aikata wa, ” a cewar sa.
Shehu ya bayyana cewar duk wanda bashi da wata mummunar manufa a kan zabukan da za a gudanar, kalaman Buhari ba za su dame shi ba.

A cewar sa, “ kalaman Buhari ba za su tayar da hankalin duk mai son a yi zabe sahihi kuma mai tsafta ba. ”

Friday, 15 February 2019

Babbar magana: An kama wasu mutane biyu yayinda suke shuka bam a  babbar gadarnan ta  Ebonyi

Babbar magana: An kama wasu mutane biyu yayinda suke shuka bam a babbar gadarnan ta Ebonyi

Babbar magana: An kama wasu mutane biyu yayinda suke shuka bam a  babbar gadarnan ta  Ebonyi


Rahotanni sun kawo cewa an kama wasu mutane biyu a jihar Ebonyi yayinda suke dana bam, a gadar Idembia da ke karamar hukumar Ezza South na jihar.

Gwamna David Umahi ya bayyana hakan a wani jawabi na musamman kan lamarin tsaro ga mutanen jihar a ranar Juma’a, 15 ga watan Fabrairu.

Yace kamun ya biyo bayan rahotannin kwararru cewa wasu mambobi na wata jam’iyyar siyasa na shirin dana bam a kan gadar da wasu wurare a jihar.
Yace wasu mazauna kauyen da ke kusa da gadar wanda ya sada Ezza South da karamar hukumar Ohaozara ne suka kama mutanen biyu.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa dan takarar kiujerar majalisar dokokin kasa na wata jam’iyyar siyasa, yan kwanaki da suka shige ya je wani waje a jihar domin siyan bama-bamai amma masu aiki a wajen suka ki amsa bukatunsa inda suka sanar da gwamnatin jihar

A wani lamari na daban, mun ji cewa kalla mutane 66 ne aka kashe a wasu unguwani da ke kusa da kauyen Maro Gida da ke karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna a wani hari da aka kai a daren jiya.

Cikin wadanda aka kashe akwai yara 22 da kuma mata 12 yayin jami'an tsaro sun ceto rayyukan wasu mutane hudu da suka jikkata kuma suna nan suka karbar magani a asibiti.

Rugagen da aka kai harin sun hada da Ruga Bahago, Ruga Daku, Ruga Ori, Ruga Haruna, Ruga Yukka Abubakar, Ruga Duni Kadiri, Ruga Shewuka and Ruga Shuaibu Yau.
Tofa! INEC za ta yi amfani da jakuna da kekuna wajen raba kayan zabe a Gombe

Tofa! INEC za ta yi amfani da jakuna da kekuna wajen raba kayan zabe a Gombe


Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC za ta dauki hayan jakuna da kekunan hawa domin amfani da su wurin rabar da kayayakin zabe a wuraren da ke ta wahalar zuwa a wasu sassan jihar Gombe.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Kwamishinan zabe na jihar, Alhaji Umar Ibrahim a wata hira da ya yi da manema labarai a garin Gombe a ranar Juma'a.
Ibrahim ya ce wuraren da ke da wahalar zuwa a suna kauyuka ne da ke kananan hukumomin Yamaltu-Deba da Shingom duk a jihar ta Gombe.

"Za mu dauki hayan jakuna da kekunan hawa da babura domin rabar da kayayakin zabe

"Hakan ya zama dole ne saboda rashin hanyoyin mota shiyasa INEC tayi tanadi da shirye-shiryen yadda za a isar da kayayakin zabe zuwa wuraren," inji shi.

Ibrahim ya ce hukumar tayi tanadi da ya dace a fanin samar da tsaro kuma ta wayar da kan masu kada kuri'a.
Ya kuma ce anyi tanadin takardun kada kuri'a na brail da makafi za suyi amfani dashi kuma kutare suna iya amfani da kafarsu domin dangwala zaben.

Har ila yau, Ibrahim ya kuma ce hukumar zaben tayi tanadin gilashi mai kara girman abubuwa ga wadanda ke fama da ciwon ido saboda su kada kuri'an cikin sauki.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa kwamishinan zaben ya ce hukumar ta tanadi na'urar da za tayi amfani da shi domin ganin yadda zaben ke tafiya tare da kuma samar da mutane masu sanya ido a kan zabe.
 An kashe mutane 66 a wasu unguwani a jihar Kaduna

An kashe mutane 66 a wasu unguwani a jihar Kaduna
A kalla mutane 66 ne aka kashe a wasu unguwani da ke kusa da kauyen Maro Gida da ke karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna a wani hari da aka kai a daren jiya.

Cikin wadanda aka kashe akwai yara 22 da kuma mata 12 yayin jami'an tsaro sun ceto rayyukan wasu mutane hudu da suka jikkata kuma suna nan suka karbar magani a asibiti.

Rugagen da aka kai harin sun hada da Ruga Bahago, Ruga Daku, Ruga Ori, Ruga Haruna, Ruga Yukka Abubakar, Ruga Duni Kadiri, Ruga Shewuka and Ruga Shuaibu Yau.


Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da afkuwar harin cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun gwamnan jihar, Samuel Aruwan. A cikin sanarwar, gwamnan ya yi tir da harin da aka kai kuma ya gargadi al'ummar akan daukan doka a hanunsu.

Gwamnatin ta ce ta tura jami'an tsaro zuwa yankin kuma an fara kama wadansu da ake zarginsu da hannu a cikin harin.

"Gwamnatin jihar ta mika ta'aziyarta ga iyalan wadanda suka mutu. An kuma tura jami'an tsaro zuwa garin har ma an kama wasu da ake zargi da hannu a harin," a cewar gwamnatin jihar.

"Ana gudanar da bincike a kan harin kuma babu shakka za a binciko wadanda suka aikata harin a hukunta su.
"Muna kira da mazauna garin Kaduna su kasance masu zama lafiya domin samun gudanar da zabe a cikin lumana da kwanciyar hankali," inji gwamnati

Saturday, 9 February 2019

sarakunan Arewa 20 sun bude katafaren masallacin Borno da akayi shekaru 32 ana gininsa

sarakunan Arewa 20 sun bude katafaren masallacin Borno da akayi shekaru 32 ana gininsaA ranar Juma'a 8 ga watan Fabrairu ne Sultan na Sokoto, Muhammad Abubakar na III na jagoranci sarakunan Arewa 20 a wurin taron kaddamar da babban masallacin garin Borno.

An kafa tuballin ginin masallacin ne shekaru 32 da suka gabata kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sultan din tare da Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi da wasu sarakuna daga arewacin Najeriya ne suka hallarci taron bude masallacin.

Masallacin da ke kusa da fadan Shehun Borno an fara ginin sa ne a 1986 bayan an rushe masallacin da ke wurin.

An kiyasta kudin ginin masallacin mai daukar mutane 10,000 ne a kan zunzurutun kudi Naira Miliyan 800.

Sai dai saboda rashin isasun kudi, an dakatar da aikin ginin ne yayin da aka kammala kashi 65 cikin 100 na aikin.
Bayan ya dare kan kujerar mulki, Shehun Borno na 20, Abubakar El-Kanemi ne ya fara neman tallafi daga al'umma domin ganin an kammala ginin masallacin.

An cigaba da aikin masallacin ne a 2011 yayin da wani fitaccen dan siyasa a jihar Borno kuma dan takarar kujerar gwamna sau biyu, Kashim Imam ya bayar da tallafin kudi Naira Miliyan 200 domin cigaba da aikin.

Daga bisani kuma gwamnatin jihar Borno ta dauki nauyin cigaba da aikin har zuwa bara da aka karasa aikin masallacin.
A jawabin da ya yi wurin bude masallacin, Shehun Borno ya ce ya na alfaharin cewa a zamaninsa ne aka kammala ginin masallacin.

Ya mika godiyarsa ga gwamnan jihar, Kashim Shettima saboda irin babbar gudunmawar da ya bayar.

Ya ce, "wannan ba irin masallacin da aka saba ginawa bane; domin cibiya ne na binciken ilimin addinin musulunci, haka ya dace a rika tsara masallatan mu; wurin ibada da kuma cibiyar ilimi."

Da farko, kwamishinan harkokin addini na jihar, Mustafa Fannarambe ya ce an samar da ababen zamani a masallacin wanda suka hada da, dakin taro, dakin karatu,

transiforma mai karfin 500kva, janareta mai karfin 200kva, manyan tankunan ruwa takwas, gini da zai dauki mutane 10,000 da kuma harabar masallaci da zai dauki mutane 5,000."

Babban Al'amari: Miji ya kashe kan sa bayan ya kwara wa matar sa ruwan guba

Babban Al'amari: Miji ya kashe kan sa bayan ya kwara wa matar sa ruwan guba

Babban Al'amari: Miji ya kashe kan sa bayan ya kwara wa matar sa ruwan guba


Wani magidanci, Daniel Okafor, mai matsakaitan shekaru ya kashe kan sa bayan an yi zargin cewar ya watsa wa matar sa wani wani ruwa mai guba a garin Nsugbe da ke jihar Anambra.

Marigayin, dan asalin garin na Nsugbe, ya hallaka kan sa ne da misalign karfe 2:30 na dare bayan ya kwankwadi ruwan gubar da ya kwara wa matar sa,

Majiyar mu ta shaida mana cewar Okafor ya fusata ne bayan ya gano cewar matar sa Paulina ta saka sunan dan su a matsayin wanda zai ci gadon gidan da ta gina,

Wani mazaunin garin Nsugbe da bai yarda a ambaci sunan sa bay a ce,

“ ya kai farmaki kan matar sa ne saboda ta saka sunan dan su a matsayin wanda zai ci gadon gidan da ta gina.

“Bayan ya gano cewar ba shine zai ci gadon gidan ba, sai ya watsa ma ta ruwan guba kuma shi ma ya sha ruwan gubar.
“Mutumin yam utu yau, Laraba, da safe yayin da ita kuma matar sa aka garzaya da ita zuwa asibiti. ”

Da ya ke tabbatar da faruwar da lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra, Haruna Mohammed, ya ce gawar Okafor na ajiye a dakin ajiye gawa,

“A ranar 6 ga watan Fabarairu na shekarar 2019 ne aka kai rahoto ofishin rundunar ‘yan sanda na 3-3 da ke Onitsha cewar wa wani mai suna Daniel Okafor ya watsa wa matar sa mai suna Paulina ruwan guba.

“Jami’an rundunar ‘yan sanda na ofishin 3-3 sun garzaya zuwa gidan ma’auratan kuma sun yi nasarar garzaya wa da Paulina zuwa Immaculate Heart Hospital domin ceto rayuwar ta.

“Shi kan sa wanda ake zargi da aikata laifin, jami’an mu sun same shi cikin mawuyacin hali kuma sun garzaya da shi zuwa asibitin Multi Care domin a duba lafiyar sa.

“Likitan asibitin ya tabbatar mana da cewar ya sha irin gubar da ya watsa wa matar sa ne .”

Mohammed ya kara da cewa daga baya likita ya tabbatar ma su da cewar Okafor ya mutu yayin da ake kokarin ceton rayuwar sa kuma an ajiye gawar a mutuware domin gudanar da wasu gwaje-gwaje a kan ta.

Thursday, 7 February 2019

Babbbar magana: Wani matashi mai shekara 27 zai kai iyayensa kotu saboda sun haife shi.

Babbbar magana: Wani matashi mai shekara 27 zai kai iyayensa kotu saboda sun haife shi.

Babbbar magana: Wani matashi mai shekara 27 zai kai iyayensa kotu saboda sun haife shi.

A wani Al'amari me kama da Almara.  Wani matashi mai shekara 27 zai kai iyayensa kotu saboda sun haife shi.

Wani mai shekaru 27 a kasar Indiya yana da shirin kai iyayensa kotu sakamakon haihuwarsa da suka yi.

Raphael Samuel dan asalin garin Mumbai ne kuma ya shaida wa BBC cewa ba daidai ba ne a ce an haifi mutum domin zai ta gwagwarmaya da wahalar duniya.

Amma Mista Samuel yana sane da cewa ba zai yiwu a nemi izinin mutum kafin a haife shi ba, amma ya dage a kan cewa "ba a nemi shawararsa ba kafin a haife shi."

Ya bayyana cewa "Tun da ba mu ce a haife mu ba, ya kamata a biya bukatunmu har karshen rayuwarmu."

Mista Samuel dai yana da wani irin ra'ayi wanda ke kyamatar haihuwa, masu irin wannan ra'ayi na Samuel suna kira ne da a dakatar da haihuwa saboda wahalar duniya.

Ya ce idan aka dakatar da haihuwa za a wayi gari babu dan adam ko daya a duniya kuma hakan zai kawo sauki ga wahalhalun duniya.

Ya ce "Babu wani alfanu a rayuwa irin ta dan adam. Mutane da dama suna shan wahala. Idan ba dan adam a duniya, dabobbi da ita kanta duniyar za su kasance cikin farin ciki."

Shekara daya da ta wuce, ya hada wani shafi a Facebook mai suna "Nihilanand," wanda ke dauke da hotunansa dauke da gemu na karya, ya rufe fuskar sa, da kuma sakwanni irin na akidarsa da ke kyamatar haihuwa.

Mista Samuel ya shaida cewa ya fara irin wannan tunanin nasa tun yana dan shekara biyar.

Ya ce "Wata rana ina yaro, abin duniya ya dame ni kuma ba na so na je makaranta amma iyaye na suka matsa sai na je. Sai na tambaye su: Me ya sa suka haife ni?' Maihafi na bai da amsar da zai ba ni, sai na yi tunanin da ya amsa tambaya ta da ba zan ci gaba tunani haka ba."

A lokacin da wannan akidar ta yi kamari a zuciyar Samuel, sai ya fito fili ya bayyana wa iyayensa irin wannan tunani nasa.
Ya ce iyayensa dukkansu biyu lauyoyi ne kuma a lokacin da ya bayyana masu abin da ke cikin zuciyarsa, sun yi na'am da wannan batu.

Mahaifiyarsa ta ce dama a ce ta hadu da shi kafin ta haife shi, da ba ta haife shi ba kuwa, domin lallai akwai hanakali a cikin wannan tunanin nasa.

Mista samuel ya ce mahaifiyarsa ta ce masa tana da kananan shekaru a lokacin da ta haife shi kuma ba ta san cewa akwai yadda za ta yi ba.

Amma abin da Samuel yake cewa, kowa yana da yadda zai yi a duniya.
A cikin wata sanarwa da mahaifiyarsa ta fitar watau Kavita Karnad Samuel ta bayyana cewa "na ji dadi da yaro na ya girma kuma ya zama bai da tsoro, kuma yana tunaninsa ba tare da wani ya tursasa ma sa ba, ina fata zai samu farin ciki a wannan hanyar da ya dauka."

Mista samuel dai ya ce wannan mataki da ya dauka na kai iyayensa kotu ya yi hakan ne a kan tuna cewa ta haka ne duniya za ta zauna lafiya ba tare da bil'adama a cikin ta ba.

Shafinsa na Facebook ya ja hankali inda ya samu tsokaci da dama. Wasu sun yaba yayin da masu adawa da shi suka ce ya je ya kashe kansa ya huta da wahalar duniya.
Wasu masu adawa da matakinsa sun ce ya yi haka ne domin neman suna a duniya.
Atiku ya girgiza magoya baya a mahaifar shugaba Buhari ta garin Daura (Hotuna Abinda yafaru)

Atiku ya girgiza magoya baya a mahaifar shugaba Buhari ta garin Daura (Hotuna Abinda yafaru)

Atiku ya girgiza magoya baya a mahaifar shugaba Buhari ta garin Daura (Hotuna Abinda yafaru)


A yayin da a yau Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci birnin Yola domin gudanara da taron sa na yakin zabe.
 kazalika Atiku Abubakar, dan takara na jam'iyyar PDP ya ziyarci garin Daura na jihar Katsina.

Ko shakka ba bu Atiku ya ziyarci mahaifar shugaba Buhari ta garin Daura, yayin da hakan ta kasance ga shugaban kasar yayin da ya kai ziyara domin gudanar da taron sa na yakin neman zabe a mahaifar babban abokin sa na adawa da ta kasance birnin Yola,

A ranar da ta gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasa ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe cikin jihar Borno da Yobe yayin da shugaban kasa Buhari ya gudanar da na sa cikin jihar Benuwe da Nasarawa.