Saturday, 25 February 2017

Addini: Mafi Tsadar Addu'o i Guda Sha Biyu (12) Da Suka Zo a Hadisi

MAFI TSADAR ADDU'O I GUDA SHA BIYU (12) DA SUKA ZO A HADISI:1. LA'ILAHA ILLAHUWA WAHADAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDA WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADIR (10 ko 100)
Manzon Allah (S.A.W) yace wanda ya fadi wannan 100 za a kankare masa zunubai dari kuma za a rubuta masa kyawawan aiki dari Kuma a wannan rana bawani da zaizo da wani aikin alheri kamar nasa sai wanda ya fadi fiye da abinda ya fada kuma za tsareshi daga sharrin shaidan da duk wani abun qi Kuma yace babu wani zikiri ko addu'a kamar Hailala


2. LA'ILLA HA ILLAHUWA MALIKUL HAQQUL MUBIN. (100)
Manzon Allah(S.A.W) yace duk wanda ya fadi wanann sau dari a rana bashi ba talauci kuma za'a tsareshi daga fitinar kabari.


3. BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM, LA HAULA WALA QUWATA ILLA BILLAHIL ALIYUL AZEEM. (100)
Manzon Allah(S.A.W) ya cewa da Sayyadina Aliyu ba wanda zai fadi wannan kalmomi duk wata masifa ko bala'i duk rintsi sai ya fita.
Annabi Alaihisalam yace wanda yake karanta Lahaula bashi ba talauci kuma kanzi ce daga kanzi na aljanna tana toshe kofofi saba'in na bala'i da cuta mafi kankanta ciki shine bacin rai da damuwa kuma yace: duk wanda samun arziki yayi masa wuya to ya yawaita yin LAHAULA...
Kuma duk wanda yake karanta BISMILLAH (21) bayan isha'i cutar annoba ko ta dauka bazata taba kamashi ba kuma bazai mutuwar fuju'a ba.


4. SUBAHANALLAHI WA BI HAMDIHI. (100)
Shine Tasbihin Annabi Nuhu shi kuma mala'iku suke Allah yake arzuta dukkan halitta dashi.


5. HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL(450)
Shine Tasbihin da Annabi Ibrahima yayi lokacin da aka jefa shi wuta Allah ya mayar masa da ita sanyi itace Sahabbai sukayi lokacin yaqin Badar Annabi yayi nasara kuma basu ji tsoron kafirai ba duk da sunfisu yawa.


6. LA ILA HA ILLA ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTU MINAL ZALIMIN (sau 41 ko 100)
Manzon Allah(S.A.W) yace: "Addu'a Annabi Yunusa lokacin da ke cikin kifi babu wani mumini da zai roki Allah wani abu dake damunsa face Allah ya maganata masa kuma yace Ismullahil Azeem sunan Allah da in Aka addu'a yake amsawa kuma idan aka rokeshi yake bayarwa itace addu'a Annabi Yunusa.


7. ASTAGFURULLAHA LAZI LA'ILA HA ILLAHUWAL HAYYUL QAYYUM WA ATUBU ILAIHI. (100)
Manzon Allah(S.A.W) yace: Ba wanda zai fadi haka fache an gafarta masa zunubansa koda sun kai kunfar kogi. kuma Alqawarin Allah ne a cikin Suratul hudu duk wanda ya lazumci Istigfari zai jiyar dashi da dadi kuma yabashi arziki kan arziki(zai samu budi) kuma zai bashi girma akan girma Daukaka.


8. SUBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBAHANALLAHIL AZEEM ASTAGFRULLAH(100 kafin Asubah)
Wani Sahabi yazo wajen Manzon Allah Alaihisalam yayi masa kukan duniya ta juya masa baya(talauci) yasanar dashi tasbihin Mala'iku sai Annabi yasanar dashi yace ya dingayi shi bayan raka'a tainul fajar kafin Asubah bai gushe ba sai da ya dawo wajen Annabi Alaihisalam yace Allah yabashi duniya (arziki) har ya rasa inda zai kaita.

9. YA HAYYU YA QAYYUMk LA'ILA HA ILLA ANTA(sau41)
Imamu Shafi'i(Rahimahullah) yayita mafarki da Annabi sai watarana sai yace shin kasanar dani wani abu da Allah zai dinga haskaka mani kuma ya raya zuciyata akan imani(ibada) sai Annabi ya sanar dashi wannan ya dingayi kafin Asubah ko bayan Asubah sau 41 (Saboda haka ba wanda zai lazumceta sai yazama mai maida hankali akan ibada kuma yazama wanda mutane zasu dinga jin maganarsa kuma abin so a cikinsu.


10. SUBAHANALLAHI(33) WAL HAMDULLAHI(33) WAL LAHU AKBAR(34) da dare kafin bacci
Wannan shine Tasbihin da Annabi ya bawa Sayyada Fatimah lokacin da ta nemi Annabi ya bata hadimi sai ua sanar da ita wannan tasbihi da ta dingayi kullum kafin ta kwanta bacci shine mafi alkhairi gareta da yabata hadimi


11. SUBAHANALLAHI(10) WALHAMDULLAHI(10) WALLAHU AKBAR(10) bayan Salloli biyar
Watarana Ummu Sulaim tazo wajen Annabi Alaihisalam tace ya sanar da ita wani abu da zata dinga rokon Allah dashi sai yace tayi wannnan tasbihin sai ta roki Allah bukatarta za ace anzartar anzartar (wato an amsa mata abinda ta roka)


12. SALATIN ANNBI (10 ko 100 ko 500 ko 1000 har abinda yayi sama)
Manzon Allah(S.A.W) yace: "wanda bukatarsa tayi masa wahalar samu to ya yawaita salati gareni lalle yana tafiyar da damuwa da bakin ciki da kuncin rayuwa kuma yana yawaita arziki da kuma biyan bukatu.

Kuma Imamu Ghazali yace: Duk wanda yake salati Annabi 500 kullum bashi talauci.....
ya ALLAH yabamu ikon kulawa....


Ku biyomu a
https://www.facebook.com/Arewarmu1
https://www.Twitter.com/Arewarmu1
https://www.Instagram.com/Arewarmu1

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

1 comment:

  1. Yakamata afasara dukan adu'oin domin mutane Susan maanoninsu.

    ReplyDelete