Monday, 20 March 2017

Ba Sani Ba Sabo: EFCC ta dirar ma tsofaffin gwamnoni 22

Kimanin gwamnoni 22 ne yanzu haka hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ke tuhuma a kotuna daban-daban a fadin kasar nan.
Shugaban hukumar na Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) na shiyyar kudu-maso-kudu Ishaq Salihu ne ya bayyana hakan ga manema labarai.


Wadanda ake tuhumar dai sun hada da Jolly Nyame na Taraba da ake zargi da satar N1.64 billion, Orji Uzor Kalu na Abia, Rasheed Ladoja na Oyo, Otunba Christopher Alao-Akala da Chimaroke Nnamani na Anambra.

Sauran kuma sune Aliyu Akwe Doma na Nasarawa, Danjuma Goje na Gombe, Ibrahim Saminu Turaki na Jigawa, Joshua Dariye na Plateau da kuma Abdullahi Adamu Nasarawa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: