Sunday, 19 March 2017

Buhari zai aikawa Gwamnoni 7 EFCC saboda sun yaudare shi

Wani babban aiki da shugaba Mohammadu Buhari zai tunkara bayan dawowarsa kan aiki, itace wata badakala da ta shafi wasu gwamnoni guda bakwai a Najeriya.

Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin ci gaba da yakar cin hanci da rashawa da yayi katutu a kasar, wannan lamari dai zai zamanto wani babban abu da shugaban zai fara tunkara, wanda ya shafi gwamnoni bakwai kan wasu rarar kudi da aka dawo da su Najeriya, daga hukumar nan mai ba da basuka ta ‘kasa da ‘kasa, wato Paris Club.


Hukumar Paris Club ta mayarwa da Najeriya zunzurutun kudi har Naira Miliyan dubu 386, daga ciki ana zargin wadansu gwamnoni guda bakwai sunyi iya kansu da kudi har Naira Miliyan dubu 19. Kuma tuni hukumar EFCC ta ce ta gano Naira MIliyan 500 da suka shiga asusun wani gwamna wanda a halin yanzu ake ci gaba da gudanar da bincike.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: