Monday, 10 July 2017

Musha Dariya: Wani Mutum Da Mahaukaci

Wanimutum ne yana cikin tafiya, toh dama akwai wani mahaukaci a gabansa sai mahaukacin ya ci karo da naira N1000 sai yayi maza ya dauke.


Sai mutumen nan ya ce masa:- “Kai Mallam Bani (ID Card) dina sai mahaukacin


Sai mahaukacin ya ce: “hehehe Haba dan Uwa in ni Mahaukacine Ai ni ba Wawa Bane.”


Toh idan ID CARD din ka ne Menene Sunanka?


Sai mutumin ya ce:-“CENTRAL BANK OF NIGERIA ”


Sai mahaukacin ya ce:- “Toh Shekarunka fa?”


Sai mutumin ya ce:-‘ “1000” ne.


Sai mahaukacin ya ce:-“Lallai Mallam ID CARD dinka ne Amshi,amma ka tabbatar kasa hoton ka nan gaba”

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

2 comments: