Thursday, 30 August 2018

Al’ajabi: Wani Uba Ya Kashe ‘Ya’yansa ‘Yan Biyu Sannan Ya Kashe Kansa

A wani lamari mai daure kai, wani uba mai shekaru 45 a duniya ya harbe ‘ya’yanshi ‘yan biyu mata masu shekaru 10 a duniya, sannan daga bisani ya juya bidigar kanshi.
Wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin a gidan mutumin da ke yankin West Rogers Park a Chicago da ke kasar Amurka.


Rahotanni sun bayyana cewa mutumin mai suna Derrick Sanders ya rabu da mahaifiyar yaran, amma su kan ziyarce shi a kowanne karshen mako.

‘Yan sanda sun samu gawar shi da misalin karfe 11:00 na safe a cikin gidan, tare da ‘yan biyun, Mason da Addison dauke da harbin bindiga a kawunansu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: