Thursday, 30 August 2018

Dalilin Da Yasa Masu Kudi Suka Fi Talakawa Son Kananan Nonuwar Mata

Wani bincike da masan suka gudanar ta gano dalilin da ya sa maza masu kudi ke son kananan nonuwar mata a yayin da su kuma talakawa ke son manya-manyan nonuwa.

Wasu likitoci 2 wadanda suka shahara a bangaren dabi’un dan Adam wato Psychologists, Viren Swami da Martin Tovée, sun gudanar da wani bincike domin gano ko arziki namiji za ta iya canza masa ra’ayinsa a kan yadda ke son girman nonon mace.


kafafen yada labarai ta Metro UK, ta ce likitocin sun gudanar da bincike ne guda 2 inda suka gwada wasu mazaje domin gano ko rashin isashen arziki (maza talakawa) za su so manya nonuwa fiye da maza masu arziki.

A binciken likitocin ta farko, sun duba alakar arziki maza da irin nonuwar da suke so. Sun dauki maza 266 daga yankuna 3 a kasar Malaysia wanda kowane daga cikin su arzikinsa ya banbanta da sauran – kadan, matsakaici da kuma sosai.

Kowane daga cikin mutanen da likitocin suka dauka an nuna masa hotunan siffofin mata wadanda nonuwan su ya duk sun banbanta. Daga nan sai aka ce kowane daga cikin su ya ya bayyana kallar da yafi ba shi sha’awa ta hanyar amfani da lamba daga 1 zuwa 5. Binciken ya nuna cewa maza masu karancin arziki (talakawa) sun fi son mata masu manyan nonuwa fiye da masu kudi.


Likittocin daga nan sai suka yi amfani da siffofin nonuwa a binciken su na 2 wanda ya nuni da asalin siffofin nonuwar mata – wanda amfaninsa shine shayar da kananan jarirai. Amma a wannan lokacin, ba su gudanar da binciken su ba a kan girman ciki ba.

Sun yi amfani da dalibai jami’a 66 masu jin yunwa, sannan kuma maza masu jin yunwa 55 wajen gwajen wannan binciken na su domin su gane ko samun isashen abinci yana da nasa gudunmawa wajen zaben maza, wadanda suka shiga a cikin shirin su shiga ko fita dakin cin abinci dalibai daga 6 na yamma zuwa 7 na yamma.

Karanta wannan: Gwamnatin Jihar Osun Ta Ware 20 Ga Watan Agusta A Matsayin Ranar Addinin Gargajiya

Sun kuma yi da amfani da fararen fata maza (wato turawa) a wajen gudanar da binciken su, domin kabila ko asalin dan Adam na daya daga cikin abubuwa da ke tasiri a zaben irin nonuwar da maza ke so.

Sannan kuma suka sake nuna hotunan wasu mata 5 masu nonuwa siffar nonuwa daban daban.Sannan kuma kamar a bayyane ya ke cewa, maza masu jin yunwa sun fi son mata masu manyan nonuwa fiye da masu kananan nonuwa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: