Friday, 3 August 2018

Wacece Hafsat Idris - Baraunuua? Kalli Tarihin ta hade da photunanta

Jaruma Hafsat Idris ta kasance tana daya daga cikin jarumain da tauraronsu je haskawa a harkar shirya fina-finai Hausa, kuma fim din da ta fara haskawa a ciki shine BARAUNIYA,
.

duk da kasancewar shi fim dinta na farko, jarumar ta samu karbuwa sosai da samun yabo daga masana harkokin finafinan.

Cikin shekara daya kacal da fara yin fim, jarumar ta zamo tauraruwar da kowane lungu da sakon ake labarinta. Gwana ce wajen iya aktin, musamman da ta kasance tana iya taka kowace irin rawa da aka dora ta.


Da farko an yi tsammanin Hafsat Idris za ta rika fitowa ne a matar aure kawai, amma daga bisani sai kwarewarta ta fito fili ta yadda take iya fitowa a finafinai kala-kala.

Babban abin da ya fi jan hankalin makallata finafinan Hausa game da jarumar shi ne, irin salon kifta idonta a lokacin da take magana.

 Wasu na ganin jarumar ta fito da nata irin salon ne domin ta kwashi magoya baya, wanda yanzu haka take samunsu a kullu yaumin.

Finafinan da suka sanya jarumar ta haye sahu na biyu a wannan jadawali sun hada da; Furuci, Dan Kurma, Maya, ‘Yar Fim, Wazeer da sauran su.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: