Wednesday, 12 September 2018

FARILLAN ALWALA, SUNNONIN ALWALA, MUSTAHABBAN ALWALA DA KUMA YADDA AKE GYARA ALWALAFarilla alwala: niyya da wanke fuska da wanke hannaye zuwa gwiwar hannu da shafar kai da wanke kafafuwa zuwa ido-sawu da cucudawa da gaggautawa.

Sunnonin alwala: wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu yayin farawa, da kurkure baki, da shaka ruwa, da fyacewa, da dawo da shafar kai, da shafar kunnuwa, da sabunta ruwa dan shafar kunnuwa, da jeranta farillai.

Mustahabban alwala: yin bisimilla, da yin asuwaki da karawa a bisa wankewa ta daya a fuska da hannaye da fara shafar kai daga goshi da jeranta sunnoni da karanta ruwa a kan gabbai da gabatar da wanke dama a kan hagu.

Ya wajaba a tsefe yatsun hannaye, an so tsefe gashin gemu mara duhu a cikin alwala amma ban da mai duhu. Ya wajaba a tsefe shi a cikin wanka ko da mai duhu ne.

Gyaran alwala:
Wanda ya manta farilla daga gabbansa na farilla, idan ya tuna a kusa sai ya wanke wannan farillar kuma ya sake wanke abinda yake bayanta, idan kuwa lokaci ya yi tsawo sai ya wanke ta ita kada ya sake sallar da ya yi kafin ya wanke din.
Idan kuma ya bar sunna sai ya wanke ta ba zai sake salla ba. Wanda ya manta gurbin da bai sami ruwa sai ya wanke shi, shi kadai ba tare da niyya ba. Idan ya riga ya yi salla kafin wannnan sai ya sake.
Wanda ya tuna kurkure baki ko shaka ruwa bayan ya fara wanke fuska, ba zai dawo zuwa gare su ba har sai ya gama alwalarsa.

::ALLAH NE KADAI MASANI.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

1 comment: