Monday, 21 January 2019

Akwai yiwuwar INEC ta dage zaben wata Jihar rives bisa wani zargi

Akwai yiwuwar INEC ta dage zaben wata Jihar rives bisa wani zargi

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta tayi karin haske dangane hukuncin da za ta yanke kan dambawar siyasar jam'iyyar APC reshen jihar Ribas. Hukumar ta ce yiwuwar gudanar zabe a jihar na da tasirin gaske dangane da hukuncin da kotu za ta zartar.

Hukumar INEC ta ce a halin yanzu hukuncin da za ta zartar na da tasirin gaske muddin jam'iyyar APC ta yi nasarar korafin da ta shigar a gaban kotun daukaka kara na haramta ma ta zabe a jihar Ribas yayin babban zaben kasa da za a gudanar a watan gobe da jibi.

Babban kwamishinan zaben reshen jihar Ribas, Obo Effanga, shine ya bayyana hakan da cewa hukumar INEC za ta dage zaben jihar muddin jam'iyyar APC ta samu kyakkyawar madogara bisa ga tsari na sahalewar hukuncin babbar kotun.

A ranar 7 ga watan Janairu, wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a garin Fatakwal, ta yi watsi da sakamakon zabukan fidda gwanayen takara na jam'iyyar APC karo biyu na kato-bayan-kato da kuma na 'yar tinke da aka gudanar a jihar Ribas.

Kotun yayin zaman da ta gudanar bisa ga jagorancin Alkali Kolawole Omotosho, ta sanyawa hukumar INEC takunkumin tsayar da kowane dan takara na jam'iyyar APC reshen jihar Ribas yayin babban zaben kasa na 2019.

an samu rabuwar kai a jam'iyyar APC reshen jihar Ribas da a halin yanzu ta bangare gida biyu yayin da kowanen su ya gudanar da na sa zaben fidda gwanayen takara da ya zamto cikas gami da hana ruwa gudu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: