Tuesday, 8 January 2019

Ko kunsan Adadin yawn mutanen da zasuyi zaben 2019 ? Ko kasan wanne yankine yafi yawan masu zabe?

Zaben 2019:
Rijistar zabe: Miliyan 84, 004, 084
Yawan mutanen da suka yi rijista a shiyyoyi shida na Najeriya:
Arewa Maso Yamma: Miliyan 20.2
Kudu Maso Yamma: Miliyan 16.3
Arewa ta Tsakiya: Miliyan 13.4
Kudu maso Kudu: Miliyan 12.9
Arewa Maso Gabas: Miliyan 11.3
Kudu Maso Gabas: Miliyan 10
Maza: Miliyan 44, 405, 439
Mata: Miliyan 39, 598,645
Legas: Miliyan 6, 570, 291
Kano: Miliyan 5,457,747
Legas: Miliyan 6, 570,291 Kano: Miliyan 5, 457,747 = Miliyan 1,112,544
Madagora: Hukumar zabe (INEC)

Hukumar zabe ta kasa watau INEC, Independent National Electoral Commission ta bayyana jimilla ta adadin 'yan Najeriya da a halin yanzu suke cikin shirin jefa kuri'un su a yayin babban zaben kasa na 2019 da za a gudanar a watan gobe.
Babbar hukumar zabe ta kasa da aka fi sani da hukumar INEC, ta bayyana cewa, a halin yanzu 'yan Najeriya miliyan 84 ke da rajista ta tabbatar da 'yancin tare cancantar kada kuri'unsu yayin babban zaben kasa na 2019.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmous Yakubu, shine ya bayar da shaidar hakan a yau Litinin yayin zaman ganawa da shugabannin jam'iyyun kasar nan cikin babban birnin tarayya na Abuja.

Cikin jawaban da Farfesa Yakubu ya gabatar, ya ce akwai Mutane 84,004,084 na adadin al'ummar kasar nan da ke da cikakkiyar cancanta ta kada kuri'un su a zaben kasa sakamakon rajistar zabe da suka riga da yi.

Wannan sanarwa ta biyo bayan tsare-tsaren da hukumar zabe ta shimfida domin babban zaben kasa da zai gudana cikin abinda bai wuci kwanaki arba'in ma su gabatowa.

Tun a bara hukumar zabe yayin fidda jadawalin ta na tsare-tsaren zabe, ta kayyade ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kujerar shugaban kasa da kuma ta 'yan majalisun dokoki na tarayya.

Kazalika hukumar ta kayyade ranar Asabar 2 ga watan Maris, 2019, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben gwamnoni da kuma 'yan majalisun dokoki na jihohin kasar nan.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, domin kyautatawa al'umma hukumar zabe ta kasa ta ce, za a ci gaba da karbar katin zabe cikin jihohi 36 da ke fadin kasar nan zuwa gabanin mako daya da gudanar zabe.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: