Thursday, 24 January 2019

Motsa jiki na kawar da cutar yawan mantuwa

Motsa jiki na kawar da cutar yawan mantuwa

Likitoci a kasar Brazil sun bayyana cewa babban abin da yake kare mutum daga kamuwa da cutar Alzheimer, wato cutar da kan sa mutum ya rika yawan mantuwa shine idan mutum ya dukufa da motsa jiki a kai akai.

Cutar Alzheimer cuta ce dake dushe kwakwalwa, sai kaga mutum na yawan mantuwa.

Likitocin sun kara da cewa bayan haka shi motsa jiki na kare mutum daga kamuwa da cutar zuciya, shanyewar bangaren jiki, rage kiba a jiki, karfafa kasusuwan jiki da sauran su.

Sannan kuma sun yi kira ga mutane da su rika motsa jikin su akalla na minti 10 a rana domin samun karin lafiya a jiki.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: