Friday, 25 January 2019

Musulmai sun yi abin a yaba masu a Kasar Amurka yayin da ake cikin wani hali

Musulmai sun raba abinci ga wadanda matsalar albashi ya shafa a Amurka

Yayin da Ma’aikatan kasar Amurka ke cigaba da fuskantar barazana daga gwamnati, mun ji labarin yadda Musulman kasar su kayi namijin kokari wajen rabawa jama’a abinci kyauta domin su samu sauki.

Musulma Amurka sun raba abinci ga wadanda matsalar albashi ya taba
Kungiyar ma’aikatan sufurin yankin Boston da sauran ma’aikatan da su ke fama da matsalar rashin albashi a dalilin rufe ayyukan gwamnati da aka yi sun samu agaji daga wasu Bayin Allah Musulmai da ke kasar Amurka a yanzu,

Wata kungiya ta musulman da ke zama a Nahiyar Amurka ce ta kawowa jama’a dauki na kayan abinci da nama na akalla Dala 20. An raba abincin ne daga wani kamfanin abinci mai suna Quincy International Foods da ke US

Akalla ma’aikata 1000 da ke aiki a filin jirgin sama na Jihar Boston wanda yanzu albashin su ya makale ne su ka amfana daga wannan sadaka da Musulmai su ka rika rabawa na kayan abinci da nama da dai sauran kayan tabawa a lashe.

Musulman sun yi alkawari cewa nan gaba za a rika raba kati da sauran abubuwan da za su ragewa jama’a radadi a daidai wannan lokaci da albashin su ya makale inji Darektan wannan kungiya ta Musulmai, Malaika McDonald,

Sama da ma’aikata 8000 da ke aiki da gwamnatin tarayya a garin Massachusetts ba su samu albashin su ba. Dole ta sa musulmai da sauran kungiyoyi su ka kawo masu agaji ganin cewa wannan abu ya shafi na kusa da su da Abokan arziki

Yanzu dai ana ta faman rikici da shugaban kasar Amurka Donald Trump da mutane inda har ta kai ma’aikata sun yi makonni kusan 5 babu labarin albashi. Yunkurin gina Katanga tsakanin Amurka da kasar Mexico ne ya jawo sabanin.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: