Saturday, 1 June 2019

Sabon gwamnan Nasarawa ya yi wasu muhimman sabbin nade-nade

Sabon gwamnan Nasarawa ya yi wasu muhimman sabbin nade-nade


Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasararwa ya yi nade-naden a karo na farko bayan darewarsa kan mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2019.
Sanarwar nadin mukamen na dauke ne cikin sakon da sakataren harkokin mulki na ofishin sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Ishaq ya fitar a ranar Asabar a garin Lafia.
Ishaq ya ce gwamnan ya amince da nadin manyan masu bawa gwamna shawara na musamman guda tara da za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuni.
Wadanda aka yiwa nadin sun hada da John Mamman, Mai bayar da shawara kan harkokin sarauta; Samuel Egya, Mai bayar da shawara na ofishin gwamna; Yakubu Kwanta, Mai bayar da shawara kan harkokin matasa da kungiyoyi masu zaman kansu; da Murtala Lamus, Mai bayar da shawara kan ayyuka na musamman.
Saura sun hada da Ibrahim Abdullahi, Mai bayar da shawara kan saka hannun jari da tsarin tattalin arziki; James Thomas, Jami'in sadarwa na Abuja; Rakiya Alaku, Mai bayar da shawara kan harkokin mata da bayar da tallafi; Salihu Ogah, Ofishin mataimakin gwamna da Abubakar Zanwa, Mai bayar da shawara kan harkokin shari'a.
Ishaq ya kuma bayyana cewa gwamnan yana son a rika kiransa da Abdullahi A. Sule.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: